Bidiyon wata kyakkyawar mace 'yar Brazil mai shekaru 27 da tsananin tsayinta mai ban mamaki ya tayar da kura a intanet. Kafar labarai na isyaku.com ya samo.
Matar mai suna Elisane Silva daga Salinopolis da ke kasar Brazil tana da tsayin kafa 6 da inci 8, Legit.ng ta tattaro.
Tun lokacin da ta yi aure da masoyinta Francinaldo Da Carvalho a cikin shekara ta 2015, matar ta shawo kan tsangwama da ba'a a kan tsayin da Allah ya halittota da shi don zama mashahuriyar Jarumar intanet.
RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI