Allah ya tona asirin mutumin da ya kashe tsohuwa mai shekara 71 ya sace kudinta bayan ya yi wa gawarta gunduwa-gunduwa


Jami’an rundunar ‘yan sandan jihar Ogun sun kama wani mutum mai shekaru 54, Dauda Bello a ranar 7 ga watan Yuli bisa zargin kashe wata mata mai suna Mesesi Adisa, ‘yar shekara 71, bayan da ya yanke ta har Lahira kuma ya yi wa gawarta gunduwa-gunduwa. Kafar labarai na isyaku.com ya samo.

An kama wanda ake zargin ne biyo bayan bacewar wanda abin ya shafa, wanda ta bar gida tun ranar 8 ga watan Yunin 2022 kuma bata dawo gida ba.

Dangin wanda abin ya shafa ta kai rahoton bacewarta a ofishin ‘yan sanda na Sabo/Ilupeju.

A ci gaba da gudanar da bincike, rundunar ‘yan sandan karkashin jagorancin SP Taiwo Opadiran, ta gano wuri na karshe da wanda abin ya shafa ta ziyarta a unguwar Olodo da ke Imala. Daga baya aka kama wanda ake zargin kuma aka kai shi ofishin Yan sanda domin gudanar da bincike.

A yayin da ake yi masa tambayoyi, wanda ake zargin ya amsa cewa ya dade da sanin wanda abin ya shafa, kuma dukkansu suna sana’ar fataucin yara. Ya ci gaba da cewa, ya gayyaci wanda abin ya shafa a wannan rana mai albarka domin tattauna harkokinsu na yau da kullum, amma da ta isa gidansa, ya gano cewa wanda aka kashe din ta zo da abin da ya ke zaton makudan kudi ne. Hakan ne ya sanya ya bugi matar da wata babbar sandar katako a kai, lamarin da ya sa matar ta sume bayan da ya dauki gawar wanda aka kashe zuwa daji.

Ya kuma kara da cewa, a lokacin da ya binciki gawar matar, ya gano cewa wadda ya kashe din tana da kudi #22,200 (Naira dubu ashirin da biyu, da dari biyu) ne kawai a tare da ita wanda ya dauke ta cikin takaici.

Ganin cewa burinsa na samun kudi da yawa a wajen wanda ya kashe din a banza ne, sai ya yanke shawarar yanke mata wuyan hannu da kuma idon sawunta, wanda ya ce an sayar da shi ga wani da ya gudu a yanzu.

Da yake tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai, kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Abimbola Oyeyemi, ya ce wanda ake zargin ya kai ‘yan sandan daji inda ya binne tsohuwar a wani kabari mara zurfi, kuma an tone gawar aka ajiye a dakin ajiyar gawa. .

Oyeyemi ya kara da cewa kwamishinan ‘yan sandan jihar, CP Lanre Bankole, ya yabawa tawagar da suka yi kwazon aiki tare da bayar da umarnin gurfanar da wanda aka kama a gaban Kotu da zarar an kammala bincike. Ya kuma ba da umarnin a gurfanar da duk wanda ke da hannu a cikin lamarin kai tsaye ko a fakaice.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN