"Suna Da Albarka": Kyawawan 'Yan Uwa Bakar Fata Sun Fito Da Dogon Gashi A Bidiyo
Bidiyon wasu kyawawan ’yan’uwa mata bakar fata suna baje kolin dogon gashi da cikar gashin kansu ya shiga intanet. Shafin isyaku.com ya samo.
A cikin faifan bidiyo mai ban al'ajabi da aka gani a Instagram, an ga 'yan uwa mata suna bi da bi don baje kolin gashin da Allah ya ba su.
A yayin da suke raba faifan bidiyon, sun yi muhawara a kan wane ne ya fi tsayin gashi a tsakaninsu. 'Yar'uwar ta farko ta ce a da ta yi tunanin nata ne mafi tsawo amma gashin 'yar uwarta ya ci gaba da girma.
Latsa kasa ka kalli bidiyo: