Hukumar tsaron farin kaya ta Najeriya NSCDC, ta tabbatar da yi wa wata yarinya ‘yar shekara biyu fyade da wasu da ake zargi da aikata fyade a karamar hukumar Yauri a jihar Kebbi. Kafar labarai na yanar gizo isyaku.com ya samo, NAN ta ruwaito.
DSC, Akeem Adeyemi, jami’in hulda da jama’a na NSCDC a jihar wanda ya tabbatar da faruwar lamarin ga Kamfanin Dillancin Labarai na NAN a Birnin Kebbi a ranar Lahadin da ta gabata, ya ce an kawo karar ne daga karamar hukumar Yauri.
“Eh, mun samu rahoton fyade ga wata yarinya ‘yar shekara biyu (an sakaya sunanta), daga jami’an mu a karamar hukumar Yauri ta jihar.
“An kama mutane biyu da ake zargi da aikata laifin fyade amma ana ci gaba da gudanar da bincike har zuwa karshensa.
"Abin da zan iya fada kenan a yanzu har sai an kammala bincike," in ji Adeyemi.
Shima da yake tabbatar da faruwar lamarin, Kodinetan Hukumar Kare Hakkokin Dan Adam ta kasa, Alhaji Hamza Wala, ya ce hukumar ta gano cewa an aikata laifin da bai dace ba akan yarinyar ‘yar shekara biyu.
“Akwai rahoton wani Likita a yankin, Dakta Bulus Godiya, babban jami’in kula da lafiya na babban asibitin Yauri, wanda ya tabbatar da cewa an yi luwadi da yarinyar ne, kuma yanzu an dauke ta zuwa cibiyar kula da lafiya ta Kalgo domin yi mata magani da samar da magunguna.
“Ba hukumarmu kadai ba, hatta kungiyoyin kare hakkin mata, kamar kungiyar ci gaban Mata ta Yauri, da kwamitin Hisbah, da sauran su, duk suna da hannu wajen ganin an yi wa wadanda ake zargin adalci, bayan an kammala bincike,” inji shi.
Ita ma shugabar kungiyar ci gaban mata ta Yauri (YWDA) Hajiya Fatima Musa-Bature ta tabbatar da faruwar lamarin, inda ta ce lamarin ya faru ne a ranar Laraba, 29 ga watan Yuni, inda ta ce bincike zai yi cikakken bayani kan komai.
Da yake magana kan lamarin, mahaifin wanda aka cutar, (an sakaya sunansa) shi ma ya tabbatar da abin da ya faru da ‘yar tasa.
"Ya faru da 'yata, amma ba zan iya yin magana da yawa a kan hakan ba yanzu."