Da dumi-dumi: Jerin gwanon motocin Gwamnan Arewa sun yi hatsari a Abuja


Jerin gwanon motocin gwamnan jihar Benuwai, Samuel Ortom, a ranar Lahadi, wani hatsari ya rutsa da su a babban birnin tarayya Abuja.

Leadership ta rahoto cewa tawagar motocin gwamnan na kan hanyarsu ta komawa Makurɗi, babban birnin jihar Benuwai bayan sun raka gwamnan filin jirgi don ya kama hanyar zuwa Birtaniya yayin da hatsarin ya faru.

Rahoto ya nuna cewa wata Motar Golf ce ta yi taho mu gama da ɗaya daga cikin motocin jami'ak tsaro da ke cikin jerin gwanon motocin gwamna Ortom.

A wata sanarwa da babban mai taimaka wa gwamnan ta fannin yaɗa labarai, Terver Akase, ya bayyana cewa babu wanda ya rasa rayuwarsa sanadiyyar haɗarin.

Ya ce lamarin ya auku ne lokacin jerin gwanon motocin suke kan hanyar koma wa jihar Benuwai bayan raka mai girma gwamna filin tashi da saukar jiragen sama na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja

A kan hanyar ne ɗaya daga cikin jerin motocin ta yi karo da wata motar Golf a kusa da gadar Nyanya a birnin tarayya.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN