Dan takarar Gwamnan jihar Sokoto na jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ya zabi Alhaji Idris Gobir, a matsayin mataimakinsa a zaben 2023. Shafin labarai na yanar gizo isyaku.com ya samo.
NAN ta wallafa cewa Alhaji Isa Sadiq-Achida, shugaban jam’iyyar APC na jihar ya bayyana haka a wani taron manema labarai ranar Talata a Sokoto.
Sadiq-Achida ya ce an zabi Gobir ne bayan tattaunawa da masu ruwa da tsaki a jam’iyyar.
Ya ce an zabi Gobir ne bisa dimbin gogewarsa da tarihinsa na siyasa.
“Kwararren mai gudanar da mulki ne, dan takararmu na Mataimakin Gwamna, ya fara aikin yi a matsayin Malamin makaranta, kafin ya tsunduma cikin sauran ayyukan gwamnati.
“Wannan ya hada da masana’antun ruwa da man fetur, inda ya yi aiki da hukumar kula da tashoshin jiragen ruwa ta Najeriya da ma’aikatar albarkatun man fetur.
“Amma a siyasa, Gobir ya taba rike mukamin kwamishinan kasafin kudi da tsare-tsare na tattalin arziki, sannan kuma ya taba rike mukamin shugaban karamar hukumar Sabon Birni ta jihar,” inji shi.
Shugaban ya ce Gobir na daya daga cikin ’yan siyasa masu son ci gaban jihar nan.
“Hakan ne don ci gaba da jajircewarsa wajen kare muradun al’ummar jihar Sakkwato, musamman a yakin da ake fama da rashin tsaro a shiyyar gabashin jiharmu,” inji shi.
A jawabinsa, Gobir, ya yabawa Sen. Aliyu Wamakko, dan takarar Gwamna na jam'iyyar APC da sauran masu ruwa da tsaki bisa ganin ya cancanci wannan matsayi.
Ya kuma bada tabbacin tabbatar da nasarar jam’iyyar a zaben 2023 mai zuwa