Daga karshe: Tinubu ya zabi abokin takararsa, duba yankin da ya fito da addininsa


Sanata Bola Ahmed Tinubu, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC a zaben 2023 ya yanke shawarar zabin abokin takararsa. Kafar labarai mai zaman kansa na yanar gizo isyaku.com ya samo.

Wata majiya mai karfi a kungiyar yakin neman zaben Tinubu da ta bukaci a sakaya sunanta ta tabbatar wa kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) a ranar Lahadi a Abuja.

Majiyar ta ce Tinubu zai bayyana sunan dan takarar a wannan makon.

“Mai yiwuwa wanda aka zaba mataimakin shugaban kasa ya kasance tsohon Gwamna ne kuma Sanata daga yankin Arewa maso Gabashin Najeriya.

“Mutumin kuma Musulmi ne, yana mai tabbatar da abin da Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano ya fada a ranar Asabar da ta gabata na cewa Tinubu ya amince da tikitin takarar Musulmi da Musulmi,” inji majiyar.

Majiyar ta kara da cewa wajen zabar abokin takarar, Tinubu bai yi tunanin addini ba, sai dai yana tunanin cancanta, da zurfin tunani na dan takarar.

Majiyar ta ci gaba da cewa: “Abin da aka yi la’akari da batun zaben wanda zai yi takara ya zo ne ta hanyar zabar mutumin da zai iya yin aiki da dan takarar shugaban kasa domin kai Najeriya ga wani matsayi mai girma.

A ranar Lahadi ne Tinubu zai kai ziyarar Sallah ga Shugaban kasa Muhammadu Buhari a Daura jihar Katsina, domin yi masa bayani kan zababben abokin takararsa.

Tsohon Gwamnan jihar Legas wanda ya yi wa’adi biyu ya lashe tikitin takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC a babban taron jam’iyyar na kasa da na shugaban kasa da aka gudanar a ranar 8 ga watan Yuni.

A baya dai ya zabi Ibrahim Kabiru Masari a matsayin wanda zai tsaya takarar mataimakin shugaban kasa.

Tinubu dai ya tafi kasar Faransa ne tun daga ranar 27 ga watan Yuni a wani dan gajeren hutu inda ya gudanar da wasu tarurrukan dabaru. Ya dawo Najeriya da sanyin safiyar Asabar domin gudanar da bukukuwan Sallah

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN