Da duminsa: An kama saurayi turmi-tabarya yana yi wa mata mai tabin hankali fyade a jihar Arewa, yadda ta faru


Rundunar ‘yan sanda ta cafke wani matashi mai suna Haruna Musa dan shekara 21, wanda aka kama yana lalata da wata mata mai tabin hankali a Angwan Gwari Kwamba da ke karamar hukumar Suleja ta jihar Neja a daren ranar Talata. Shafin isyaku.com ya samo.

A cikin faifan bidiyon da Daily trust ta samu, an ji Musa yana cewa har yanzu bai shiga ba kafin ihun matar ya sanar da mutane.

Musa, wanda aka same shi da kullin kayan da ake kyautata zaton tabar wiwi ne, ya dora laifin shaye-shaye da kuma tsinuwa daga kauyensu. Ya kara da cewa matar tana tsirara ne sakamakon haka hankalinsa ya bi.

Yace; 

 “Ba don jami’an tsaro ba, da wata kila zan yi lalata da ita. Ban san abin da ya zo mini ba. Don Allah a yafe ni. Ni kawai shekara 21 ne. Ina da abubuwa da yawa a raina. Matsalolina sun fi ni girma. Ba ni da wanda zai taimake ni.”

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN