DA DUMI-DUMI: 'Yan bindiga sun kai wa tawagar Shugaba Buhari hari a Katsina


Wasu ‘yan bindiga a ranar Talata, 5 ga watan Yuli, sun bude wuta kan ayarin motocin shugaban kasa Muhammadu Buhari a jihar Katsina
. Legit.ng ta ruwaito

A cewar mai magana da yawun shugaban kasa, Garba Shehu, dan Najeriya na daya ba ya cikin ayarin a lokacin da aka kai harin, amma jami’an tsaro da tawagar da suka nufi Daura mahaifar Buhari, gabanin Sallah, an kai musu hari a kusa da Dutsinma a Katsina.

Ya ce, "masu gadin fadar shugaban kasa ne suka dakile harin".

“Fadar shugaban kasa ta bayyana a matsayin abin bakin ciki da rashin jin dadi, lamarin harbin da ya faru a kusa da Dutsinma, jihar Katsina, a kan ayarin motocin da ke dauke da jami’an tsaro da jami’an tsaro na Advance Team, Protocol da kuma jami’an yada labarai gabanin tafiyar shugaban kasa, Muhammadu Buhari zuwa Daura domin yin Sallah.

Maharan sun bude wa ayarin motocin wuta ne daga inda suka yi musu kwanton bauna amma sojoji da ‘yan sanda da jami’an DSS da ke tare da ayarin sun dakile.

“Mutane biyu da ke cikin ayarin motocin suna karbar magani kan kananan raunukan da suka samu. Duk sauran ma’aikata, da ababan hawa sun isa Daura lafiya.”

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN