Akalla jirage masu zaman kansu 11 ne suka dira birnin Maiduguri domin daurin auren Shehu dan tsohon shugaban Najeriya (Bidiyo-Hotuna)


Akalla jirage masu zaman kansu 11 ne suka isa birnin Maiduguri na jihar Borno domin daurin auren Shehu dan tsohon shugaban Najeriya Marigayi Umar Musa 'Yar'adua. Shafin isyaku.com ya samo.

A yau 23 ga watan Yuli ne Shehu zai daura aure da Amaryarsa Yacine diyar Hon. Mohammed Nur Sheriff.


Shehu Dan shekara 29, ya Sami Digirinsa na farko a fannin tattalin arziki a Jami'ar Schellhammer da ke kasar Spain, yayin da ya yi Digirinsa na biyu a Jami'ar Webster da ke kasar Netherlands.

Amaryarsa Yacine, mai shekara 22 ta sami Digirinta na farko a Jami'ar Surrey da ke kasar Ingila.



Latsa kasa ka kalli bidiyo

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN