Wani sabon rikici ya barke a jam’iyyar All Progressives Congress (APC), yayin da dubban ‘ya’yan jam’iyyar mai mulki a ranar Alhamis, 21 ga watan Yuli, suka sauya sheka zuwa jam’iyyar adawa ta PDP a garin Gulma da ke karkashin karamar hukumar Argungu ta jihar Kebbi. Shafin isyaku.com ya samo.
Legit.ng ta ruwaito cewa wadanda suka sauya sheka sun samu jagorancin Alhaji Mansur Adamu Gulma Yargyra, tsohon jigo a jam’iyyar APC a jihar, inji rahoton The Nation.
Masu sauya sheka daga APC sun bada dalilai
A madadin wadanda suka sauya sheka daga jihar Kebbi, Mansur ya ce ya bar jam’iyyar APC mai mulki ne sakamakon rashin adalci da wasu masu son kai da ba su kaunar jam’iyyar a zuci suke yi wa da yawa daga cikin ‘ya’yan jam’iyyar.