Daga Mukhtar A. Haliru Tambuwal Sokoto
Zamu cigaba da fafatukar nemawa Almajirai, karatun Allo da Tsangayoyi hakkin su da samar da dokar kafa Hukumar kula da inganta tsarin karatun Allo, Tsangaya da Almajirci da kuma shigo da tsarin inganta tattalin arzikin kasa Nigeria ta hanyar amfani da manhaja da dubaru da tsarin Zakka da Waqafi, a Majilisar Dokokin Tarayya, inji Dan Majlisa Hon. Balarae Shehu Kakale Shuni.
Dan Majilisar Dokokin Tarayya mai wakiltar kananin hukumomin Bodinga,Dange-Shuni da Tureta daga Sakkwato, wanda kuma mamba ne na kwamitin Maigirma Shugaban Kasa na gyaran tsarin ilimi zabi da kanka a Nigeria, ya bayyana anniyar sa ta cigaba da fafatukar kwatowa Almajirrai hakkin su, a mataki na kasa da jihohi baki daya.
Hon. Kakale wanda yaje Majilisar karo na farko, ya bayyana cewa son karatun kur'ani ne, gyara tsarin Tsangaya, dogaro da kai, tarbiyar alumma, zaman lafiya da inganta tattalin arzikin kasa yasa ya tsunduma cikin lamurran Almajirrai.
Bugu da kari dan Majalisar ya bukaci hadaka da Hukumar Ilimin harshen larabci da Ilimin Addinin Musulunci (Sokoto Arabic and Islamic Education Board) da Hukumar Zakkat da Waqafi (SOZECOM) na jihar Sokoto domin suyi kokarin inganta harkar Almajirrai da kuma taimakawa Mutane yankin sa, domin inganta harkar Kasuwanci,Noma, harkar lafiya, muamalar bankunan Musulunci da basu da ruwa da sauran su.
Wannan ya bada damar zagaya daukacin Gundumomin sa, da tattaunawa da mutanen sa, a karshe aka samar da dinbin kayan tallafin dan Dogaro da kai da habaka Kasuwanci da inganta shaanin Lafiya.
Yanzu haka sun samar da kungiya mai mambobin a Majilisar Dattawa da Wakilai, ya zayarci jahohi daban daban dan wannan fafatukar. Ya bayyana cewa babu hujjar hanawa Almajirrai Hakkin su da makaranta Allo alhali ana baiwa wasu bangarorin da ba su kai su muhimmanci ba.
Hon. Kakale dan Majilisa ne da ya sanya Almajirrai jirgin sama daga Sokoto yaje da da su har zauren Majalisa domin kariyar kudurin na sa.
A kwanan baya dai dan Majilisar ya raba dinbin kayayyaki ga Malammai da Limamai yankin sa da mahardata kur'ani da sauran Al'ummah dan amfana da wakilci na gari.