Allah ya yi wa wata mata mai suna Aisha Ahmed rasuwa a Makkah na kasar Saudiya sakamakon wani rashin lafiya da ba a bayyana ba.
Aisha yar karamar hukumar Keffi ne a jihar Nassarawa tarayyar Najeriya.
Sakataren zartarwa na hukumar kula da jin dadin Alhazai na jihar Nassarawa Idris Al-Makura ya ce Aisha ta rasu ranar Laraba 29 ga watan Yuni bayan gajeruwar rashin lafiya.
Rubuta ra ayin ka