Yan banga sun yi wani bajinta a Kogi, sun ceto mutum biyu bayan artabu da wasu miyagu (Hotuna)


A ranar Lahadin da ta gabata ne kungiyar ‘yan banga a Kogi ta tarwatsa gungun masu garkuwa da mutane, inda suka kashe biyu daga cikin masu laifin tare da kubutar da wasu mutane biyu da aka sace. Kafar labarai ta yanar gizo isyaku.com ya samo.

NAN ta ruwaito cewa wadanda aka ceton sun hada da Mallam Sanni Uwaiti da Ramatu Tukur.

An kuma kwato makamai da alburusai na masu garkuwa da mutane.

Mista Abdulrahaman Ohiare, shugaban karamar hukumar Okehi ta Kogi, ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a Lokoja ta hannun mataimakinsa na musamman, Mista King Habib.

Ohiare ya ce masu garkuwa da mutanen biyu sun gamu da ruwan nasu ne a yayin wani samame da wata tawagar ‘yan banga da mafarauta suka kai a safiyar ranar 26 ga watan Yuni.

“Daya daga cikin masu garkuwar ya mutu ne a lokacin da suka yi artabu da ‘yan bangan, yayin da daya kuma wanda ya samu munanan raunuka ya mutu a hanyar zuwa asibiti.

“Kungiyar ta dade tana addabar masu ababen hawa a kan titin Okene zuwa Lokoja da kuma titin Okene-Auchi na jihar Kogi kafin a kai masu farmakin.

"Da sanyin safiyar yau ne aka yi nasarar kubutar da wasu mutane biyu da aka yi garkuwa da su a tsaunin Upogoro dake Okehi," in ji shi.

Shugaban karamar hukumar ya bayyana cewa an gudanar da aikin ne a matsayin martani ga umarnin da Gwamna Yahaya Bello ya bayar ga shugaban karamar hukumar na yin aiki tare da tabbatar da tsaro a karamar hukumar Okehi da kewaye.

Ya ce majalisar ba za ta bar wani abu ba a yunkurinta na tsarkake karamar hukumar Okehi daga duk wani nau’i na laifuka.

Ya kara da cewa majalisar ta yabawa Bello bisa la’akari da tsaron rayuka da dukiyoyin ‘yan jihar Kogi a matsayin babban fifikon gwamnatin sa.


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN