Jam’iyyar APC ta na marmarin Kwankwaso ya dawo, ta ce zai iya rike Najeriya nan gaba


Mataimakin sakataren yada labarai na jam’iyyar APC na kasa, Yakubu Ajaka ya yi kira ga Rabiu Musa Kwankwaso ya dawo APC da ya bari.

A wata hira da aka yi da Yakubu Ajaka, ya nuna cewa a halin yanzu Rabiu Musa Kwankwaso ba zai iya lashe zabe ba. Vanguard ta fitar da wannan rahoto.

Ajaka ya shaidawa manema labarai a garin Abuja cewa ba zai yiwu NNPP ta karbi shugabancin kasa ba, don haka zai yi kyau Kwankwaso ya sake tunani.

A cewar mataimakin kakakin na APC mai mulki, tsohon gwamnan na jihar Kano ya taka rawar gani sosai wajen nasarar da jam’iyyar ta samu a zaben 2015.

Ina ma ya dawo APC

Daily Nigerian ta rahoto Ajaka yana mai cewa jagororin jam’iyyar APC sun yi niyyar yi wa Kwankwaso sakayyar irin abin da ya yi masu a wancan lokaci.

Sai dai sakataren yada labaran na APC ya ce ba zai yiwu a taimakawa Sanata Kwankwaso a yanzu da ya sauya-sheka zuwa wata jam’iyyar hamayya ba.

Ba a zama shugaban kasa a NNPP

“Shiyasa na ce bai makara da dawowa APC ba. Asali da nan ya fi dacewa, kuma yana da tabbacin zama shugaban kasa wata rana, ba kamar NNPP dinsa da ta yi suna a wani bangare kurum ba.”

“Ko da yake wasu mutane su na yaudararsa, har su na kiran shi Shugaban kasa, amma mutum ba zai iya karbar shugabancin Najeriya daga kuri’un jiha daya ko biyu a Arewa maso yamma ba.”

“Kwankwaso yana bukatar jam’iyyar da ta ratsa kasa irin APC domin ya cin ma burinsa na yin mulki. Saboda haka ina kiran shi da ya yi abin da ya kamata, tun kafin lokaci ya kure masa.”

- Yakubu Ajaka

Makomar Peter Obi da Atiku

Da aka tambayi Ajaka a game da Peter Obi, sai ya nuna cewa idan an buga gangar siyasa, mutane za su gane bambancin APC da jam’iyyar adawa irin Labor Party.

Ajaka yana ganin ana zuga tsohon gwamnan na Anambra ne a kafofin sada zumunta na zamani.

A game da Atiku Abubakar kuwa, Ajaka yake cewa APC ta saba doke PDP, don haka iyakar Atiku ya zo na biyu, ma’ana Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ne zai ci zabe.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN