Wani shaidan gani da ido ya yi zargin cewa ‘yan bindigar da suka kai hari kan ayarin motocin Alhazai a Sokoto sun kashe ‘yan sanda 6.
Mahajjatan da ke kan hanyarsu ta zuwa Sokoto domin zuwa Saudiya wajen gudanar da aikin Hajji, an kai musu hari ne a dajin Gundumi. Daga baya aka dawo da su Gadar Sarkin Gobir Isa ba tare da jin rauni ba.
Wani mazaunin garin Isa da ya nemi a sakaya sunansa ya shaida wa Daily trust cewa ‘yan ta’addan sun kashe ‘yan sanda shida.
Yace;
“’Yan bindigar sun yi wa ayarin motocin kwanton bauna ne karkashin jagorancin ‘yan sandan tafi da gidanka. Jami’an da ke gaban su ne suka yi artabu da ‘yan bindigar wanda hakan ne ya sanya Alhazan suka tsere yayin da motocinsu suka koma Isa”.
Lamarin dai ya tilastawa hukumar jin dadin Alhazai ta jihar dage tashin tashin su zuwa ranar Laraba saboda tun da farko an umarce su da ya tashi da karfe 7:30 na safiyar ranar Talata.
Rubuta ra ayin ka