Wani mutum ya kwada wa Minista mari a wajen ibada, jami'an tsaro sun murkushe shi



Yan sanda a Uganda sun kama wani mutum mai shekaru 39 da laifin marin karamin Ministan ayyuka da sufuri na kasar, Mista Musa Ecweru. Kafar labarai na yanar gizo isyaku.com ya samo.

An tattaro cewa mutumin ya mari Ministan ne a lokacin da ake gudanar da taro a Cocin St. Michael Catholic Church da ke gundumar Wera a gundumar Amuria ranar Lahadi, 26 ga watan Yuni. 

Ana zargin cewa Ministan wanda kuma dan Majalisar Wakilai ne na gundumar Amuria, yana halartar addu’o’i a Cocin, sai Mista Michael Okurut, mazaunin Wera ya kai masa hari.

Rahotanni sun ce Ministan ya je ya kai wata tarakta da ma’aikatar noma ta mika wa Cocin Katolika na Wera ne.

Majiyoyin da lamarin ya faru a idonsu da misalin karfe 11:30 na safe sun shaida wa Daily Monitor cewa Okurut cikin nutsuwa ya shiga ginin Cocin inda ya zarce zuwa bangaren inda yake Wanda ya shagaltu da yi wa jama'a bayani kuma ya kawada masa Mari.

"Ya zo a hankali har ma ya yi alamar giciye. Ina tsammanin zai sami kansa wurin zama kamar yadda sauran 'yan ikilisiya suke yi amma sai ya tafi wurin Ministan ya rada masa wani abu kafin ya mare shi a kunne." wata majiya ta ce.

"Ya yi yunkurin marin Ministan karo na biyu amma sai Minista ya tare hannunsa kafin masu rakiya da ke jiransa daga waje suka garzaya cikin Cocin suka murkushe shi (Okuru). Majiyar ta kara da cewa. 

Mista Oscar Ageca, mukaddashin mai magana da yawun ‘yan sanda na gabashin Kyoga, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin a ranar Litinin, ya ce an kama Okurut, aka kai shi ofishin ‘yan sanda na Wera domin yi masa tambayoyi.

"An bude shari'ar cin zarafi a ofishin 'yan sanda na Wera inda aka nadi bayanai kuma an tsare wanda ake zargin saboda ana gaggauta bincike kan lamarin," in ji Mista Ageca.

Da aka tuntubi Mista Ecweru, ya bayyana wanda ake zargin a matsayin mai tabin hankali.

"Mun gano bayanansa na asali, mun tabbatar da cewa Mahaukaci ne, haukansa yakan kai masa hari lokaci-lokaci kuma idan ya sha wahala yakan kasance mai tashin hankali" in ji Mista Ecweru.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN