Alkali ya ki sauraron karar Lauya saboda sanya tufafin 'Limamin juju' zuwa kotu, wai domin Kotun koli ta halalta sa Hijabi a Makarantu


Wata babbar Kotun tarayya da ke Legas ta ki sauraron kararrakin da Lauyan kare hakkin dan Adam, Malcolm Omirhobo, ya shigar a gaban Kotun sanye da rigar Malamin addinin gargakiya “Juju Priest”. Kafar labarai na yanar gizo isyaku.com ya samo.

A ranar Alhamis din da ta gabata, Omirhobo ya halarci zaman kotun koli sanye da tufafi kamar Limamin juju. Yana da farin alli wanda aka zana akan kwas ɗin idonsa ɗaya, yana da sarƙoƙin ƙafafu, sannan kuma ya ɗaurab jan kyalle a kugunsa, kuma yana da fuka-fukan tsuntsu a kansa.

Omorhibo ya shaidawa manema labarai cewa yana amfani da ‘yancinsa na asali ne biyo bayan hukuncin da kotun koli ta yanke na kwanan nan wanda ya tabbatar da sanya Hijabi a makarantu.

A ranar Litinin, 27 ga watan Yuni, Lauyan ya gurfana gaban Alkali Tijani Ringim, ya yi irin wannan shigar wanda ya haifar da martani daga wasu Lauyoyin da suka ce ba a saurare shi ba. An kusa tsayar da shi a bakin kofar shiga harabar Kotu saboda adon sa amma ya shige ciki yana gardama.

Karan Omirhobo na farko mai lamba FHC/L/CS/929/2022 ya shigar kan gwamnatin tarayyar Najeriya da sauran su yayin da karar ta biyu; FHC/L/CS/1392/2021, ya shigar kqn Sojojin Najeriya da wasu mutane biyu.

Da aka kawo kararsa gaban Alkali, aka ki amincewa da shi, sai Omorhibo ya ce;


“Ya Mai shari'a , dokokin ba za su iya maye gurbin tsarin mulkin Tarayyar Najeriya ba.

Bayan sauraron gardamar tasa, Mai shari’a Ringim ya umurci Omirhobo da ya yi jawabi ga kotu kan dalilin da ya sa za a saurare shi yadda ya kaya a ranar da za a dage zamansa.

Kotun ta ba da umarnin cewa kada rubutaccen jawabin nasa ya wuce shafuka biyar tare da madogarun hukunci da aka ambata, ta kara da cewa dole ne a shigar da shi kafin ranar da aka dage sauraron karar.

“Ba za ka iya magana dlga Jotu haka nan a matsayin kwararre ba. Zan dage shari’ar ka kuma ka zo ka yi magana a Kotu idan doka ta ba ka damar bayyana a kotu kamar yin irin wannan shiga haka a Kotu,” in ji Alkalin.

Alkalin kotun ya dage sauraron karar zuwa ranar 10 ga Oktoba, 2022.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN