Tinubu zai fice daga APC nan ba da dadewa ba? Tsohon Gwamnan Kudu maso Yamma ya bude lamarin, ya bada bayani


Wani tsohon Gwamnan jihar Ekiti, Segun Oni ya karyata ikirarin cewa jagoran jam'iyyar APC na kasa, Bola Tinubu zai fice daga jam'iyyar. 

Daily trust ta ruwaito cewa Oni ya bayyana irin wannan ikirarin na cewa Tinubu zai koma jam’iyyar Social Democratic Party (SDP) ne saboda akwai shirye-shiryen da APC ke yi na hana shi tikitin takarar shugaban kasa a 2023 a matsayin hasashe kawai. 

Da yake magana da manema labarai a Abuja a ranar Laraba, 1 ga watan Yuni, bayan kaddamar da kwamitin karamin taro na SDP, Oni ya amince cewa SDP a bude take ga mutanen da suke da ra’ayi da manufa daya da jam’iyyar. 

Ya kara da cewa wadanda suke shirye su zurfafa dimokaradiyya da shugabanci na gari a tsarin siyasar Najeriya ana  maraba da zuwansu jam’iyyar. 

Kalamansa: 

“Yawan hasashe! Bari in ce mu Social Democratic Party ne. Dangane da abin da ya shafi kofofinmu a bude suke ga kowa da kowa. Ba muna kulle dama a nan ba. Zamu jira. 

"Kowane tsari za a dauki shi da mahimmanci kuma ba tare da wani fifiko ba. Don haka, kar a yi hasashe da nisa. Za mu yi taron mu.” 

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN