Wata Tsohuwa Yar shekara 105 mai suna Mrs Felicia Fayomi ta sami fitowa ta kada kuri'a ranar Asabar 18 ga watan Yuni lokacin zaben Gwamnan jihar Ekiti.
Karkashin kulawar Jikarta, tsohuwar ta je ta kada kuri'arta a mazaba ta biyu Wad na shida (Unit 2, Ward 6) a garin Ifaki Ekiti da ke karamar hukumar Ido-osi.
Bayan kada kuri'arta, tsohuwar ta ce:
"Na gode wa Allah na kada kuri'a ta".