Likita ya kwada wa ma'aikaciyar jinya mari a dakin jinya cikin Asibiti, duba abin da ya biyo baya


Kungiyar ma’aikatan jinya da ungozoma ta kasa (NANNM), reshen babban birnin tarayya Abuja, ta bukaci a yi adalci a kan wani hari da aka kaiwa mamban ta, Nurse Ebalu Marvis na asibitin kasa da ke Abuja.

Shugaban kungiyar, Kwamared Deborah Yusuf, a lokacin da take zantawa da manema labarai a ranar Juma’a a Abuja, ta yi zargin cewa Dokta Atinko-Sunday Ikeya na wannan asibitin ya afkawa Marvis, yayin da take hidima ga majinyata a asibitin.

Shugaban ta yi zargin cewa a ranar 13 ga watan Yuni, Ikeya ya yi watsi da duk wata ka’ida ta likitanci da kuma sana’a don cin zarafin ma’aikaciyar jinya da ke aiki a matsayin abokin aikinsa a asibitin.

A cewar Yusuf, Likitan da ake zargi ya dage cewa dole ne ma’aikaciyar jinya ta bar majinyacin da ta ke yi wa hidima domin yin suturar raunin wani mara lafiya a sashin kula da lafiyar mata.

Ta bayyana cewa bayanin da ma'aikaciyar jinya Marvis ta yiwa likitan cewa tana kula da majiyyaci a kan ciyarwar Naso Gastric tube. Sai dai ya ki yarda da hakan.

“Atinko ya shiga ya ce, “Madam ke ce ke tafiyar da wannan majinyatan? Me yasa raunin wannan majiyyaci ba a yi dressing ba?” Ta gaya masa cewa likitocin O da G ne ke gyara raunin.

"Wadannan likitocin tun da farko sun zo ne a cikin 'yan mintoci kaÉ—an da suka gabata don yin suturar amma majiyyacin yana cikin sashin dialysis, haka ma fakitin suturar ba a samu ba.

“Dr Atinko ya fara yi mata tsawa yana cewa Madam zo ki yi ma wannan mara lafiyar dressing ciwonta yanzu. Dan uwan ​​Ukamaka Godwin ya amsa cewa likitocin da ke sashen O and G sun ce za su yi suturar.

“Ma’aikaciyar jinya ta kara da cewa likitocin O da G ne suka gyara raunin a ranar da ta gabata, amma idan ya nace a bar shi ya rubuta.

“Maimakon rubutawa a takardan kundin aiki, sai ya matso kusa da ita ya ce Madam na ce ki je yanzu ki yi dressing’, amma ta ce masa wannan trolley din magani ne banda dressing pack din babu shi.

"Atinko ya ci gaba da tsare Marvis wanda ke kan tukin trolley din magani daga cikin dakin. Abu na gaba da ya biyo baya za a iya tunanin wani mugun yanayi ne kawai a cikin wani fim mai ban tsoro yayin da ya mari ta,” in ji Yusuf.

Shugaban ta bayyana cewa ma’aikaciyar jinyar ta amsa wa likitan ne ta hanyar tambayarsa me ta yi da ya sa aka yi mata mari, kuma a lokacin ne ma’aikaciyar jinyar ta fahimci warin barasa daga bakin maharin.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN