Siyasar Kebbi: Tsintsiya ta kama da wuta a jihar Kebbi, duba dalili


Jam'iyar APC mai mulki a jihar Kebbi na ci gaba da tafka asarar magoya bayantta yan tsagin tsohon Gwamnan jihar Kebbi Adamu Aliero inda akalla mutum Miliyan daya Mata da yaran iyalan magoya bayan tsohon Gwamnan suka ci gaba da ficewa daga jam'iyar APC cewar Umar Namashaya Diggi
.

Tuni sabani tsakanin bukatun wasu jiga-jigai a jam'iyar APC reshen jihar Kebbi ya kai ga ballewar Adamu Aliero zuwa jam'iyar PDP mai adawa, lamari da ya sa dubu-dubatan magoya bayansa suka bi uban gidan su zuwa jam'iya PDP.

Mun tattaro cewa Adamu Aliero ya sani daidaito da jam'iyar PDP a jihar Kebbi kuma har an aminta bisa manufa da aminci kan wasu mukamai da aka ba shi da jama'arsa, 

Kafin wannan mataki, jiga-jigan yan jam'iyar APC dai sun jaye daga takarar fidda gwani na jam'iyar APC a jihar Kebbi bisa mabanbantan dalilai. Daga bisani kuma aka sani guguwar canja sheka zuwa jam'iya PDP a jihar Kebbi.

Yayin da hakan ke faruwa, jam'iyar APC ta yi shiru duk da cewa Adamu Aliero ya saki faya fayin bidiyo a Facebook har guda biyu da suka kalubalanci jam'iyar APC da martabar Gwamna Bagudu, amma har yanzu jam'iyar APC ta yi ta kurma kan lamarin.


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN