Da dumi-dumi: Rikici ya barke tsakanin Hausawa da Inyamurai yan kasuwa a Edo, wasu sun jikkata, jami'an tsaro sun karbe yankin


An samu barkewar rikici a safiyar ranar Asabar, 11 ga watan Yuni a garin Benin, jihar Edo, yayin da fusatattun matasa wadanda yawancinsu yan kasuwa ne a sabuwar kasuwar Benin suka tashi hankali bayan wani dan kasuwa daga arewa ya farma takwaransa na Igbo da adda.

Rigima ya fara ne bayan wani dan sabani da ya shiga tsakanin yan kasuwar biyu. An ce dan Igbon ya umurci Bahaushen da ya bar masa gaban shagonsa, jaridar Punch ta rahoto.

An tattaro cewa ana haka ne sai Bahaushen dan kasuwan wanda hakan bai yi masa dadi ba ya zaro addansa sannan ya caki Inyamurin.

Wani bidiyo da ke yawo a shafin soshiyal midiya ya nuno fusatattun matasan suna zanga-zanga yayin da suka farma wanda ake zargi da aikata kisan kan.

Jaridar Punch ta kuma rahoto cewa tawagar tsaro na hadin gwiwa da suka hada da sojoji da yan sanda sun karbe yankin da lamarin ya afku.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN