Gidauniyar Qatar ta gina wa Iyalai 150 yan gudun hijira gidaje na zamani a Sokoto


Akalla iyalai 150 ‘yan gudun hijira a jihar Sokoto ne a ranar Asabar din da ta gabata aka raba musu dakunan kwana na zamani wanda gidauniyar Qatar Charity Foundation ta bayar.

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa aikin na daya daga cikin ayyukan da gidauniyar Qatar Charity Foundation ta yi a Sokoto, wadda ta ci gaba da tallafawa mabukata a jihar.

Tallafin gidauniyar tare da hadin gwiwar hukumar zakka da bayar da kyauta ta jihar Sokoto, ya yi tasiri matuka ga rayuwar dubban iyalai a jihar.

Da yake kaddamar da rukunin gidajen Rahama 150 ga ‘yan gudun hijira a garin Gandi da ke karamar hukumar Rabah, Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar, ya yaba wa wadanda suka bayar da gudunmawar.

Gwamna Aminu Tambuwal na jihar, ya bayyana bikin a matsayin daya daga cikin nasarorin da gwamnatin sa ta samu.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN