
Jihar Zamfara za ta fara yanke wa masu garkuwa da Yan bindiga hukuncin kisa
June 28, 2022
Comment
Abdullahi Shinkafi, mashawarci na musamman kan harkoki tsakanin hukumomin gwamnati ga gwamnan Zamfara, ya ce Majalisar Dokokin Jihar ta amince da kudin dokar hukuncin kisa ga yan bindiga, rahoton The Cable.
Yau, gwamna zai rattaba hannu kan dokar hukuncin kisa ga masu garkuwa, masu kai musu bayanai da sauran laifuka masu alaka da yan bindiga," in ji shi.
"Majalisar dokokin jihar, a jiya a Zamfara ta amince da dokar hukuncin kisa ga masu garkuwa da mutane, masu kai musu bayanai da masu basu gudunmawa."
0 Response to "Jihar Zamfara za ta fara yanke wa masu garkuwa da Yan bindiga hukuncin kisa"
Post a Comment
Rubuta ra ayin ka