Hukumar NSCDC ta kama wani dan banga sakamakon yi wa yarinya ‘yar shekara 13 mugun aiki a jihar arewa


Rundunar ‘yan sandan farin kaya da jami’an tsaron farin kaya a jihar Nasarawa ta cafke  wani jami’in ‘yan banga mai suna Yusuf Dallah dan shekaru 45 da haihuwa bisa  zarginsa da lalata wata yarinya ‘yar shekara 13 mai suna Ummi a jihar.

Da yake gabatar da wanda ake zargin a gaban manema labarai, jami’in hulda da jama’a na NSCDC, Jerry Victor, ya ce karamar yarinya mai suna Ummulkhulthum Musa, wadda ake zargin ta saci wasu atamfofin zannuwa, an kama ta zuwa ofishin ‘yan banga da ke hanyar Jos a cikin Lafia. Shugaban ‘yan sandan ya ce an kawo yarinyar ofishin ‘yan banga ne bisa zargin sata da ake yi mata, kuma Yusuf ya yi amfani da damar da karamar yarinya ke hannunsu tare da lalata ta.

A cewar kakakin rundunar NSCDC, bayan da rundunar ta yi masa tambayoyi lokacin da ake bincike, Yusuf ya amsa laifinsa.

“An kama wanda ake zargin Yusuf Dallah aka kawo ofishinmu domin yi masa tambayoyi da bincike lokacin da wadda aka lalata ta kai rahoton lamarin ga yayanta wanda daga baya ya sanar da hukumar NSCDC wanda ya dauki matakin da ya sa aka kama wanda ake zargin.

Da aka yi hira da shi, wanda ake zargin ya musanta aikata laifin da ake zarginsa da shi, sannan ya ce bincike zai ‘yantar da shi yayin da Ummulkhulthum Musa  ta dage cewa wanda ake zargin ya yi mata fyade

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN