Bayanai da ke fitowa daga fagen siyasar jihar Kebbi na nuna cewa nan ba da dadewa ba wani babban dan siyasa tare da wasu yan Majalisar Dokoki na jihar Kebbi guda shida za su canja sheka daga jam'iyar APC zuwa PDP.
Lamari da masana harkokin siyasa a jihar Kebbi ke wa kallon mataki na biyu na kasancewa babban kamu da jam'iyar adawa ta PDP za ta yi a kasa da kwana 30.
Kafar labarai na intanet isyaku.com ya samo cewa ana mataki na tattunawa da wannan babban dan siyasa, wanda ake yi wa kallon babbar ginshiki siyasar yankin da ya fito a jihar Kebbi.