Jami’an rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna sun kashe ‘yan bindiga hudu a Saminaka da ke karamar hukumar Lere a jihar.
‘Yan sandan sun kuma kwato bindigu kirar AK47 da Ak49 dauke da alburusai masu rai da kuma wata motar aiki da ‘yan fashin ke amfani da su.