Boka ya kira Yan sanda su kama mutumin da ya kawo yayansa biyu domin a yi masa tsafin samun kudi, duba abin da ya faru


Wani faifan bidiyo da yake zagaya a yanar gizo ya nuna ‘yan sandan da wani Boka ya kira su domin su kama wani mutum da ke son sadaukar da ‘ya’yansa biyu don tsafin yin kudi a Ghana.

Bokan mai suna Oyibi, Nana Adu-Boafo, ya gayyaci ‘yan sanda domin kama mahaifin yara 12 mai suna Evans Oppong.

An ce wanda ake zargin ya dauko diyarsa ne a makaranta yayin da ake ci gaba da karatu, inda kai tsaye ya nufi gidan Bokan domin gudanar da ibadar tsafi domin ya sami kudi. Wanda ake zargin ya yi ikirarin cewa ya dawo ne daga kasar waje, an ce ya ziyarci gidan wani Boka mai suna Nana Adu-Boafo inda ya nemi a yi masa tsafi domin ya sami arziki. 

Oppong ya kuma yi alkawarin sadaukar da 'ya'yansa biyu don aiwatar da tsafin samun zarziki. 

Yan sanda sun cafke shi kuma sun fara gudanar da bincike.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN