Da dumi-dumi: PDP za ta sake zaben fidda gwani a jihohi hudu da wasu mazabun tarayya, ta sa rana


 Jam’iyyar PDP ta amince da sake zaben fidda gwani a mazabar tarayya da na Jihohi na jihohin Legas, Imo, Benue da Katsina domin tantance ‘yan takara a zaben 2023 mai zuwa. NAN ta ruwaito.

Jam’iyyar ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ta fitar a daren Juma’a ta hannun sakataren yada labaranta na kasa, Debo Ologunagba, a Abuja.

Shafin labarai ta yanar gizo na isyaku.com ya tattaro cewa Ologunagba ya ce bayan tattaunawa mai zurfi kan rahotannin kwamitin zabe da daukaka kara kan majalissar PDP a jihohin Legas, Imo, Benue da Katsina, kwamitin ayyuka na kasa (NWC) ya amince da sake zaben fidda gwani.

Ya ce hukumar ta NWC ta amince da ranar Lahadi 5 ga watan Yuni domin sake zaben fidda gwani a mazabar Ahiazu da Orsu na jihar Imo; da kuma Musawa, Dandume, Zango dake jihar Katsina.

Sauran a cewarsa sun hada da: Mazabun tarayya na Oru East/Orsu/Orlu, da Kwande/Ushongo na jihar Benue.

Haka kuma a ranar litinin 6 ga watan Yuni domin gudanar da zaben fidda gwani na majalisar wakilai ta jihar Legas (Mazabu 24 na tarayya).

“Bugu da kari kuma, Sanatan Kaduna ta tsakiya a jihar Kaduna, Sanatan Enugu ta Yamma na jihar Enugu da kuma mazabar tarayya ta Boki/Ikom da kuma mazabar Jahar Yakuur II, dukkansu na Cross River da aka shirya yi a ranar Asabar 4 ga watan Yuni an soke su,” inji shi.

Ya shawarci daukacin ‘ya’yan jam’iyyar na jihohin da abin ya shafa da su lura da sabbin ranakun.

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN