2023: Atiku ya shiga tsaka mai wuya bayan jigon PDP a Kudu ya ce har abada ba zai goyi bayansa ba


Tsohon gwamnan jihar Ekiti, Ayo Peter Fayose, ya yi bayanin abin da ya sa Nyesom Wike ba zai taba goyon bayan Atiku Abubakar a zaben 2023 ba.

A wata hira da Premium Times ta yi da Ayo Peter Fayose, ya fadi dalilin Gwamna Nyesom Wike na juya baya ga ‘dan takaran na PDP a zaben shugaban kasa.

Fayose ya kara nanata matsayarsa na cewa bayan Muhammadu Buhari ya kammala shekara takwas, abin da ya kamata shi ne shugabanci ya koma kudu.

Bugu da kari, ‘dan siyasar ya ce Atiku Abubakar ya yi alkawarin zai zabi Gwamnan na Ribas a matsayin abokin takara, amma daga baya ya canza magana.

Atiku ya ci amanar Wike?

An rahoto Fayose yana ikirarin Atiku ya yi wa Wike alkawari shi zai zama ‘dan takarar mataimakin shugaban kasa bayan gama zaben tsaida gwani.

Daga baya sai aka ji ‘dan takaran ya yi watsi da Gwamna Wike, ya dauko Gwamna Ifeanyi Okowa.

Wike bai taba cewa yana son mataimakin shugaban kasa ba, amma lokacin da Atiku ya kai masa ziyara, shi ne ya ce 'ina so ka zama mataimaki na.'”

“Shi (Atiku) ya fadawa Wike wannan, idan har ya canza magana, shin bai kamata ya sanar da Gwamna Wike ba? Bai dace Wike ya samu labari ba?”

- Ayo Fayose

Mu na tare da Wike 100%

Ko me zai faru a PDP, tsohon gwamnan ya ce ba zai ci amanar Wike ba, ya ce yana tare da shi dari bisa dari, yake cewar domin da kudi Wike aka tafiyar da jam’iyya.

“An yi wa Wike illa, amma za mu cigaba da zama da shi. Duk abin da ya yi, haka za mu yi; duk inda ya fada mana mu je, can za mu tafi.”

“Wike ba zai taba cewa mu goyi bayan Atiku ba. Na kalubalance shi a kan wannan. Idan Wike ya ce mu bi Atiku, to za mu yi watsi da shi.”

- Ayo Fayose

Ba a dauki maganar kwamiti ba

A hirar da aka yi da shi ta waya, Fayose ya kara da cewa Atiku ya yi watsi da shawarar da kwamitin da PDP ta nada a kan batun takarar 2023, ta gabatar masa.

“PDP ta kafa kwamiti da zai bada shawarar wa zai zama abokin takara, wanda kwamitin suka zaba shi ne Wike, amma ba ayi aiki da maganar ba.”

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN