An kama wani Bawan Allah da ya gina gida da shafukan Alkur'an a Kano


Rundunar Hisbah da ke kokarin tabbatar da bin dokokin Musulunci a Kano ta ce ta cafke wasu mutane uku da take zargin sun yi amfani da shafukan littafi mai tsarki wajen yin gini.

BBC Hausa ta rahoto cewa waɗan da ake zargin sun yi amfani da wasu shafukan Alƙur'ani mai tsarki ne wajen gina gida a Anguwar Gaida ta jihar Kano.

Mataimakin rundunar yan sandan Musuluncin mai kula da sashin ayyuka na musamman, Ustaz Usaini Usman Ceɗiyar Ƴan Kuɗa, ya shaida wa manema labari cewa sun kama me gidan da Malamin da ya ba shi fatawar hakan.

Ya ƙara da cewa yayin da dakarun Hisbah suka dira wurin, sun ga an kwaɓa Simintin gini da irin waɗan nan takardu na wani sashin Littafin Allah mai tsarki.

Mutane sun rushe gidan

A jawabinsa da wakilin jaridar, Ustaz Usaini ya ce tuni ma'aikatan da ke aikin ginin da wasu mazauna anguwan suka rushe gidan baki ɗaya.

Ya ce:

"Mun kama me gidan da Malamin da ya ba shi fatawar yin haka. Mutumin ya faɗa mana yana haka ne don samun tsaro, shi kuma Malamin ya ce ya amince a yi haka ne saboda me gidan ɗalibinsa ne."

"Ma'aikatan da ke aikin akasarin su basu san me aka yi ba da farko, da wasu mutane sun rushe gidan, kuma lokacin da jami'ai suka isa sun ga ana kwaɓa yashi da takardun."

Mataimakin shugaban ya ce a halin yanzun suna cigaba da gudanar da bincike kuma da izinin Allah da zaran sun gama zasu miƙa lamarin ga hukuma ta gaba don ɗaukar mataki.

Tsohon kwamishinan ayyuka da tsare-tsare na jihar Kano, Muaz Magaji, ya aike da sakon neman yaf iy a ga gwamna Ganduje.

Injiniya Magaji, wanda aka fi sani da Ɗan Sarauniya ya samu saɓani da gwamnan ne bayan yin wani rubutu a Facebook da ya taɓa kimar Ganduje.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN