Zamfara: 'Yan bindiga sun kai wasika bayan kashe manoma 7 da wani limami


Wasu ‘yan ta’adda sun kashe akalla manoma 7 da babban limamin masallacin Juma’a na garin Faru mai suna Malam Sani Akwala a ranar Asabar, a kauyen Dajin Danau da ke kauyen Faru a karamar hukumar Maradun a jihar Zamfara. Legit ta ruwaito.

An kai harin ne da misalin karfe 12:45 na rana lokacin da 'yan ta'adda kusan 30 dauke da makamai suka kai farmaki a gonakin da ke Faru, wanda ke da nisan kasa da kilomita daya.

‘Yan ta'addan sun hadu da manoman ne a lokacin da suke aikin sassabe a gonakinsu. Da ganinsu, sai wasu manoman suka gudu domin tsira da rayukansu.

Saidu Bala Faru, wani ganau da ya tsallake rijiya da baya, ya shaida wa HumAngle cewa:

Muna gonakinmu saboda an yi ruwan sama kamar da bakin kwarya a jiya (Juma’a), kwatsam sai ga shi wadanan ‘yan ta’adda dauke da makamai sun fara harbin mutanen mu.

“Daga cikin manoma bakwai da aka kashe yayin harin akwai Sani Abdullahi, Muhammad Mani Na-Umma, Mala, Sani Na-Akwala, da Muhammad Lauwali Yar-Tusgi.”

Adnan Katara, wani manomi, ya ce:

“Dukkan mutanen bakwai da aka kashe, shugabannin gidajensu ne… sun bar yara sama da 49 a matsayin marayu da za su tagayyara a kauyen.”

Ibrahim Isah ya ci gaba da shaida wa HumAngle cewa ’yan bindigan sun afkawa kauyukan da ke karkashin gundumar Faru suna neman kudin fansa kan ayyukan noma a yankunan.

A wata wasika da kungiyar ta’addancin ta rubuta kuma ta kai wa hakimin kauyen, ‘yan ta’addan sun ce:

“Babu wani aikin noma da za a yi a yankin a lokacin damunan bana har sai an cimma matsaya kan harajin noma.”

Isah ya kara da cewa:

"Kungiyar ta'addancin na zagayawa gonaki-gonaki domin tabbatar da bin umarninsu."

Ya koka da cewa zai yi wahala manoma a wannan daminar su yi noma, ya kuma yi kira ga hukumomi da su gaggauta yin wani abu.

Kokarin jin ta bakin mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara, SP Mohammed Shehu ya ci tura saboda ba a iya samunsa ta wayar tarho ba.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN