Wata mata da ba a gane ko wace ba ta haifi Jariri kuma ta gudu ta barshi a garin Sapele na jihar Delta.
Majiyar mu a garin Sapele ta ce ranar Juma'a 27 ga watan Mayu matar ta haifi Jaririn ne tare da taimakon wata Tsohuwa. Sai dai daga bisana aka nemi uwar Jaririn aka rasa domin ta tsere.
An kai Jaririn gidan Marayu na Testimony Orphanage a hanyar Shell Road, hannun riga da wajen shakatawa na Uduaghan Park.
Rubuta ra ayin ka