Ukraine ta kwace Karkhiv daga sojojin Rasha


Mazauna birnin Kharkiv na kasar Ukraine sun fara komawa gidajensu bayan sojojin Rasha da suka yi yunkurin mamaye birnin sun janye. Aminiya ta ruwaito.

Gwammnan Kharkiv da ke Gabashin Ukraine, Oleh Synyehubov, ya ce sojojin kasar na ci gaba da kora dakarun Rasha, a yayin da mazauna birnin da suka tsere saboda yakin suka fara komawa gidajensu.

Duk da haka, Synyehubov, ya yi gargadi cewa yanayin na da hadari, don haka jama’a da su rika rika yin la’akari da yanayin tsaronsu kafin su dawo birnin da zama.

A cewarsa, sojojin Rasha sun dasa nakiyoyi masu tarin yawa a yankin, kafin su janye.

Synyehubov ya kuma ce dakarun na Rasha ba su kai hari a birnin Kharkiv ba, sai dai wasu kauyuka da ke yankin.

“Saboda haka bai kamata a yi saurin sakin jiki ba, don haka ina kira ga jama’a da su yi gaggawar yin abin da ya dace da zarar sun ji sanarwa ko wata alama, sannan su daina fita kan tituna sai idan ya zama dole,” inji shi.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN