Da Dumi: Zanga-Zanga ta ɓarke a Sakkwato kan kama mutanen da suka kashe Debora


Mutane sun ɓarke da zanga-zanga kan tituna a wasu sassan jihar Sokoto ranar Asabar kan kama wasu da ake zargin su da kashe ɗalibar da ta yi batanci ga Annabi (SAW).

Daily Trust ta rahoto cewa wata ɗaliba yar aji biyu a makarantar horar da malamai ta Shehu Shagari, Debora Samuel, ta rasa rayuwarta hannun jama'a bisa zargin ta zagi Annabi Muhammad (SAW).

Mutanen da suka fito zanga-zangar sun ɗaga Alluna da aka yi rubuta daban-daban kamar, "ku sako yan uwan mu Musulmai," "Musulmai ba yan ta'adda bane," da sauran su.

Ku dakaci karin bayani...

Previous Post Next Post

Information

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun Labaran mu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/J8ryqryDtwR9yvxrOOBlJU

Domin zama wakilinmu a garinku LATSA NAN

Korafi ko aiko labari LATSA NAN