Al'ummar Hausawa mazana Lagos sun bukaci Gwamna Babajide Sanwo-olu ya janye umarnin hana yin Acaba a kananan hukumomi shida na jihar su kuma al'umma Hausawa su tula masa kuri'u lokacin zabe.
Shugabannin Hausawa sun shaida wa Gwamnan cewa al'ummar Hausawa mazauna Lagos suna da dimbin yawa lamari da ya sa su kan gaba cikin al'umma da ke ba da yawancin kuri'u lokacin zabe a Lagos.
Gwamna Babajide ya sanya dokar hana Acaba a kananan hukumomi shida biyo bayan kashe wani mutum da Yan Acaba suka yi sakamakon gardama kan N100 na kudin Acaba.
Rubuta ra ayin ka