Yan sanda sun budewa masu garkuwa da mutane wuta, sun halaka 3 a jihar Adamawa


Rundunar 'yan sandan jihar Adamawa ta bayyana yadda jami'an ta suka halaka wasu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne guda uku, gami da cafke wasu biyu, sannan suka tseratar da wani da aka yi garkuwa da shi guda daya yayin da suka kai samame tare da mafarauta a karamar hukumar Fufore dake jihar.

Suleiman Nguroji, kakakin rundunar ne ya sanar da hakan wata takarda da ya fitar ranar Alhamis a Yola, Premium Times ta ruwaito.

Ya bayyana yadda lamarin ya auku a ranar 17 ga watan Mayu, a tsaunin Sambo, wanda ke tsakanin yankin Chigari da anguwan Gurin.

"An yi nasara a samamen da jami'an rundunar 'yan sandan marabar Gurin da manoman tsaunin Sambo, wanda ke tsakanin Chigari da dagacin Gurin cikin karamar hukumar Fufore suka kai.

"Sakamakon wadannan nasarorin ya biyo bayan matakan da rundunar ta tsara don duba lamurran garkuwa da mutane, fashi da makami, satar shanu, munanan ayyukan 'yan bindiga, da dai sauran laifuka.

"Wandanda ake zargin masu garkuwa da mutane ne, yayin da su ka yi ido biyu da jami'anmu sun yi musayar wuta da su, a sanadin haka ne, suka sheke uku daga cikin su, tare da damko biyu," ya bayyana.

A cewarsa, samamen yayi nasarar ceto wani da aka yi garkuwa da shi, Buba Hamidu, mazaunin kauyen Samlo cikin karamar hukumar Fufore.

Wasu daga cikin hatsabiban sun tsare tare da raunukan harsasai, a cewar kakakin.

Ya kara da bayyana yadda kwamishinan 'yan sandan jihar Adamawa, Sikiru Akande, ya jinjinawa DPO marabar Gurin, wanda ke kula da lamurran Chigari da kokarin da mafarautan su ka yi.

Kwamishinan 'yan sandan ya tabbatar wa gwamnati da mazauna jihar da tabbatar da bankado mabuyar hatsabiba da wuraren ta'addancinsu a fadin jihar.

"Shugaban 'yan sandan ya umarci tawagar OC da su cigaba da bincike, sannan a tabbatar an gurfanar da wadanda ake zargin," a cewarsa.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN