An kama wani dalibi dan shekaru 19 da haihuwa da laifin dabawa wata tsohuwar masoyiyarsa kuma dalibar makarantar sakandire mai shekaru 22 wuka har lahira.
Hukumar binciken manyan laifuka ta kasar Kenya ta bayyana cewa, wani matashi dan shekara 19, mai suna Tony Kiptoo na makarantar sakandare ta Keben, ya daba wa tsohuwar masoyiyarsa Irene Chelagat wuka a gefen hagu na kirjinta, inda ya kashe ta nan take bayan ta ki amincewa da sha’anin soyayyarsa.
Jami’an makarantar sun bayyana Chelagat a matsayin daliba mai Æ™wazo kuma mai himma, wanda ta taka rawar gani a fannin da ya shafi Turanci.
Binciken da DCI ta gudanar ya nuna cewa Kiptoo ya shirya kisan Chelagat ne saboda ya yi mata fatan mutuwa sakamakon rubuta "Ki mutu lafiya" a jikin wani hotonta da DCI ta samu a dakinsa.
An kuma samu labarin cewa matasan sun samu rashin jituwa a tsakaninsu kafin su yi watsi da soyayyarsu, kuma Chelagat ta ci gaba da gudanar da rayuwarta. Duk da haka, Kiptoo ya kasa jurewa kuma ya fusata bayan ya gano cewa tsohuwar masoyiyarsa ta samo sabon "Masoyi", wanda kuma ya saya mata sabuwar wayar hannu.