A kalla mutum 21 ne suka riga mu gidan gaskiya yayin wata turereniya da aka yi da safe a wani cocin zamani a Port Harcourt, babban birnin Jihar Rivers.
Daily Trust ta rahoto cewa wani shaidan gani da ido, ya ce lamarin ya faru ne yayin bikin rabon kyauta da kayan abinci karo na hudu da cocin ta yi.
Shaidan ya ce wasu cikin bakin sun iso tun ranar Juma'a yayin da wasu suka iso misalin karfe 6.30 na safiyar ranar Asabar don taron da aka shirya farawa karfe 9 na safe.
Shaidan ya ce wasu mutane da za su yi wasannin motsa jiki sun iso haraban cocin misalin karfe 8 na safe kuma suka bude wani karamin kofa, hakan ya bawa dandazon mutanen da ke waje damar kutsawa cocin, hakan ya janyo turereniyar.
A yau da safe abin ya faru. Cocin ya gayyaci mutane wurin bikin rabon kyauta da kayan abinci karo na hudu. Wasu sun taho tun ranar Juma'a, wasu kuma suka iso tun karfe 6.30 na ranar Asabar.
"Wasu da za su yi wasannin motsa jiki sun bude wata karamar kofa sai dandazon mutanen da ke waje suka kutsa kai kuma aka yi turereniya. Na kirga kimanin gawa 21 a kasa," in ji shi.
Ya ce an garzaya da mutane da dama zuwa wani asibiti da ba a bayyana sunansa ba.
Da aka tuntube ta, Kakakin yan sandan Jihar Rivers, Iringe Grace Koko, ta ce tana hanyar zuwa wurin da abin ya faru domin samun sahihn bayani.
Saurari karin bayani ...