Malamin addinin Musulunci ya ketare rijiya da baya bayan farmakin Yan daban siyasa domin ya yi waazi cewa a zabi mutumin kirki a 2023


Wani malamin addinin Musulunci, Malam Aliyu Muhammadu Tukur, ya bayyana yadda wasu da ake zargin ‘yan bangar siyasa ne suka kai masa hari a cikin wani Masallaci da ke karamar hukumar Akko a jihar Gombe. 

Da yake bayyana wa Aminiya irin halin da ya shiga, Malam Tukur ya ce yana gudanar da Tafsiri a cikin wani Masallaci da ke kusa da gidansa makonni biyu da suka wuce, sai ‘yan barandan suka kai masa hari bisa zarginsa da yin magana kan zaben 2023 mai zuwa.

Malamin mai shekaru 42, wanda ke koyarwa da wa’azi a garin Kumo, ya ce ya yi sa’a maharan, wanda manufarsu shi ne su kashe shi, ba su yi nasara ba amma sun yi masa mummunar rauni.

Ya ce laifin da ya aikata shi ne jawabin da ya yi a lokacin rufe Tafsirin Ramadan a Masallacin sa, inda ya bukaci dalibansa da sauran mabiyansa da su zabi ’yan takarar da suka dace da suka taba rayuwarsu da ayyukan alhairi.

“Lokacin rufe tafsirin watan Ramadan a Masallacin, na yi tsokaci ne kan zabe mai zuwa, inda na bayyana cewa dalibaina da sauran mabiya za su zabi ‘yan siyasa ne kawai wadanda suka samu damar kawo ci gaban al’ummarmu,” inji shi.

“Bayan Sallah mun dawo tafsirin da muke yi kafin watan Ramadan, don haka a ranar 11 ga watan Mayu da misalin karfe 8 na dare, mintuna kadan da fara Tafsirin, sai muka ji muryoyi na tambayar a ina na zauna.

“Kafin mu fahimci abin da ke faruwa, ’yan daba kusan biyar ne suka kutsa cikin Masallaci suka zuba min fetur. Daya daga cikinsu ya jefar da wata na’urar da ta fashe kuma ta haddasa gobarar da ta kone sassan hannayena, da kujerata, da kwafin Alkur’ani da kafet a cikin Masallacin, ciki har da wasu dalibaina da su ma suka samu raunuka.”

A cewar mahaifin ‘ya’ya biyar, ya gane wasu daga cikin maharan mazauna unguwarsu ne kuma magoya bayan daya daga cikin masu neman kujerar Majalisa, ya ce ba shi da wata matsala da su, kuma bai san dalilin da ya sa aka kai masa hari ba. .

A yayin da ya yi kira ga Gwamnatin jihar da ta tashi tsaye domin magance matsalar tabarbarewar matasa a jihar, ya kara da cewa bai kamata a bar matasa da sauran wadanda ke haddasa matsala da radadin al’ummar da ba su ji ba su gani ba, ba tare da an hukunta su ba.

Da yake tabbatar da faruwar lamarin, Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, ASP Mahid Muazu Abubakar, ya ce an kama wasu mutane biyu da ake zargi da hannu a lamarin. 

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN