Duba abin da ya faru a Kotu bayan wani Mai gadi ya saci doya

 


A ranar Talata ne wata kotu da ke Jos, ta yanke wa wani mai gadi, Auwal Suleiman, mai shekaru 26, hukuncin daurin watanni shida a gidan yari, bisa samunsa da laifin satar wasu doya na mai gidansa.

Alkalan kotun Mista Ghazali Adam da Hyacenth Dolnanan, sun yanke hukuncin ne bayan wanda ake tuhumar ya amsa laifin sata tare da rokon kotun da ta yi masa sassauci.

Sun bai wa mai laifin zabin tarar N20,000.

NAN ta ruwaito cewa tun da farko, Dan sanda mai shigar da kara, Insp Monday Dabit, ya shaida wa kotun cewa, an kai karar ne ofishin ‘yan sanda na C’ Dibision Jos a ranar 5 ga Mayu, daga hannun Sagir Garba, wanda ya shigar da kara.

Ya ce Suleiman, wanda wanda ya shigar da karar ya dauke shi aiki a matsayin mai gadi amma sai ya ya saci wasu doya da aka damka masa amana. 

Dan sanda mai gabatar da kara ya shaida wa kotun cewa har yanzu ba a tantance kimar kudin doyan da aka sata ba.

Dabit ya ce laifin ya ci karo da tanadin sashe na 274 na dokar jihar Filato ta Arewacin Najeriya.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN