Kotu ta tasa keyar masu gadi 3 zuwa Kurkuku bayan sun aikata abin kunya

 


A ranar Talata ne wata kotun Majistare da ke Ota, Ogun, ta yanke wa wasu jami’an tsaro na kamfani su uku hukuncin daurin watanni uku a gidan yari bisa samun su da laifin satar kayayyakin aluminium da kudinsu ya kai Naira miliyan 2.5 mallakin ma’aikacin su
.

NAN ta ruwaito cewa Rundunar ‘yan sandan ta gurfanar da Onuh Isaac, 27, Jonathan Udoh, 33, da Solomon Adam, 32, da laifin sata da hada baki.

Wadanda aka yanke wa hukuncin, wadanda ba a bayar da adireshinsu ba, sun ki amsa laifin da ake tuhumar su.

Da yake yanke hukunci, Alkalin Kotun Mai shari’a A.O Adeyemi, ya yanke wa kowane daya daga cikin su hukuncin zaman gidan yari na tsawon watanni uku ba tare da zabin tara ba.

Adeyemi ya ce masu gabatar da kara sun tabbatar da tuhumar da ake yi ba tare da wata shakka ba.

Tun da farko, Lauyan masu gabatar da kara, EO Adaraloye, ya shaidawa kotun cewa wadanda aka yankewa hukuncin da sauran su, sun aikata laifin ne a ranar 11 ga watan Maris, da misalin karfe 1 na safe, a masana’antar Iloyds Aluminum, daura da All-over Polytechnic, Ota.

Adaraloye ya ce wadanda aka yanke wa hukuncin, kasancewar jami’an tsaron kamfanin ne, sun hada baki ne a tsakanin su inda suka sace kayayyakin aluminium da ya kai Naira miliyan 2.5, mallakin ma’aikacin su.

Mai gabatar da kara ya ce laifin ya ci karo da sashe na 508 da 516 na kundin laifuka C38, dokokin jihar Ogun,2006.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN