Magoya bayana ne suka bayar da Motoci ga ma’aikatan Khadimiyya ba APC Excos ba – Malami

Magoya bayana suna bayar da Motoci ga ma’aikatan Khadimiyya ba APC Excos ba – Malami


Babban Lauyan Tarayya kuma Ministan Shari’a, Abubakar Malami, SAN, ya ce bai bayar da kyautar mota ga duk wani Excos ko delegates na APC na Jihar Kebbi ba.

Malami ya bayyana hakan ne a wani taron tattaunawa da manema labarai a Birnin-kebbi.

Rahotanni sun nuna cewa Malami yana da magoya bayansa daga gida da waje.

Magoya bayan sa ba su tsaya kawai wajen matsa masa lamba don neman kujerar gwamnan jihar Kebbi a zabe mai zuwa ba, har ma sun bayar da gudunmawar kudi sama da N135m nan take.

“Taimakon N135m na baya-bayan nan ya bude kofa don bayar da gudummawa da tallafin kayayyaki da dama da suka hada da motoci na masu hannu da shuni,” in ji Malami.

Ya lura cewa labarin da ke danganta shi da rabon motocin ba gaskiya ba ne kuma ba a fahimta ba. 

“Kawaye da abokan aikin Malami ne suka bayar da gudummawar motoci ga ma’aikatan da suka dade suna aiki a gidauniyar Khadimiyya. 

"Bikin ba wai don rabawa masu ruwa da tsaki na jam'iyyar APC motoci ba ne, babu wani daga cikin masu ruwa da tsaki na jam'iyyar APC ko wakilai a jihar Kebbi da Malami ya ba wa kowa mota, har yanzu ban bayar da kyautar mota ga kowa ba". 

“Kuna iya tuntubar Sakatariyar jam’iyyar APC ta kasa, ku sami jerin sunayen duk masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC a jihar Kebbi, ku yi wani labarin bincike don jin ta bakinsu, sai ku gane yadda da’awar ta kasance ta gaskiya. 

“Idan aka kwatanta sunayen masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC da wadanda suka ci moriyar motar, zai bayyana muku cewa babu wata alaka tsakanin su biyun kuma ba su da alaka ko kadan,” inji shi.

Kalli bidiyoPost a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN