An banka wa wasu matasa 2 wuta aka kone su kurmus a jihar Benue, duba dalili


Fusatattun jama'a sun kashe wasu da ake zargin ‘yan fashi da makami ne a ranar Litinin 1 ga watan Mayu, suka kone su kurmus a Kanshio da ke wajen garin Makurdi a jihar Benue.

Rahotanni sun bayyana cewa barayin sun shiga wani gida a Kanshio a kokarinsu na yi wa wani iyali fashi bayan sun yi harbin lokaci-lokaci domin tsoratar da jama'a don kada su tunkare su a safiyar ranar Litinin.

Sai dai an bi su aka kama su daura da Divine Mercy Minor Seminary School dake Kanshio inda daga karshe aka banka musu wuta.

An kuma bayyana cewa yayin da aka kama biyu daga cikin wadanda ake zargin, daya ya tsere. Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Benue PPRO, SP Catherine Anene, ta tabbatar da faruwar lamarin.

Anene ta ce; 

“An tabbatar da lamarin. Ana ci gaba da bincike don Allah."

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN