Kwatsam wata gawa ta tashi ana tsakar kai ta wajen...


Wani majiyyaci na Covid, wanda aka ayyana ya mutu kuma an rufe shi a cikin jakar hawa, ya dawo da rai kafin a kona shi. Shafin labarai na isyaku.com ya tattaro.

Ma'aikatan gidan jinya sun ayyana mutumin wanda dan fansho ne cewa "ya mutu".

Hotuna daga China sun nuna ma'aikatan jinya  dauke da jakar gawar mai karbar fansho zuwa wata babbar mota don kai shi inda za a kona shi.

Duk da haka, a kan hanyarsu ta zuwa wajen motar, an ga motsi na fitowa daga jakar.

Sai suka zare jakar, suka tarar da mutumin yana motsi yana raye.

Ana iya jin wani ma'aikaci yana cewa: "Ka zo nan ka ga ko ya mutu? Har yanzu yana numfashi! Ba ka ga yana motsi ba?"

Wani ma'aikacin  ya ce: "Yana da rai, kada ku sake rufe fuskarsa."

Daga nan aka kai mutumin asibiti domin a duba lafiyarsa.

Lamarin ya faru ne a gundumar Putuo da ke birnin Shanghai a ranar Lahadi 1 ga watan Mayu, kuma an fahimci cewa hukumomi sun kaddamar da bincike na gaggawa kan yadda aka sa mutumin a cikin jakar gawa da ransa.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN