Kwastam ta kama tireloli 12 makare da buhunan shinkafar waje mai gubaHukumar Kwastam ta Zone A ta sanar da kama buhunan shinkafa 7,259 na kasar waje mai nauyin kilogiram 50, kwatankwacin manyan motoci tireka 12 a watan Afrilun 2022.

Hukumar ta ce, rundunar ta kama wasu mutane 12 da ake zargi da shio da haramtattacciyar shinkafar da sauran kayayyaki.

Da yake zantawa da manema labarai a sashin a ranar Alhamis, 5 ga Afrilu, 2022, Kwanturolan Hukumar Kwastam mai kula da sashin, Hussein Ejebunu ya bayyana cewa an gano buhunan shinkafar da ba su dace da cin dan Adam ba.

An kama wadanda ake zargi da shigo da shinkafa mai guba da sauran kayayyaki

A cewar Ejebunu, an kama mutane 12 da ake zargi da aikata wasu laifuka daban-daban da suka saba da ka'idojin kwastam.

Rahoton Punch ya bayyana cewa Ejebunu ya ce bisa tsarin gwamnatin Najeriya na karfafa noman shinkafa, sashin ya kama buhuna 7,256 na shinkafa mai nauyin kilogiram 50 wanda zai cika manyan motoci tirela 12.

Shinkafar na kunshe da abubuwa masu hadari

Ya ce binciken dakin gwaje-gwaje na NAFDAC ya tabbatar da cewa shinkafar tana da illa kuma tana dauke da wasu sinadarai masu guba da bai kamata dan Adam ya ci ba, kamar yadda ta ruwaito.

Ejebunu ya gargadi ‘yan Najeriya da su lura da wasu buhunan shinkafa da ake shigowa da su na kasashen waje, yana mai cewa ba su da lafiya ga cimar dan Adam.

The Nation ta ruwaito, Gwamnan ya sanar da hakan ne a Zaria yayin shagalin bikin gargajiya na Hawan Bariki wanda Sarkin Zazzau, Ahmad Nuhu Bamalli yayi.

Previous Post Next Post

Information

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun Labaran mu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/J8ryqryDtwR9yvxrOOBlJU

Domin zama wakilinmu a garinku LATSA NAN

Korafi ko aiko labari LATSA NAN