Kotu ta yanke wa mutumin da ya kashe Basarake a Najeriya hukuncin kisa ta hanyar rataya


Babban kotun Jihar Ekiti, a ranar Alhmis a yanke wa wani mutum, Stephen Ominiyi, hukuncin kisa ta hanyar rataya saboda kashe wani da ke jiran gadon sarauta a Ekiti, rahoton Premium Times.

Mr Omoniyi, wanda aka yi ikirarin cewa yana da matsalar tabin hankali, ya daba wa Gbadebo Olowoselu, sarkin Odo Oro Ekiti a wancan lokacin, a karamar hukumar Ikole a Augustan 2018.

Alkalin, Kayode Ogundana ya ce masu shigar da karar, karkashin jagorancin Adegboyega Morakinyo, sun gamsar da kotu cewa Mr Omoniyi ne ya kashe marigayin basaraken.

"Bayan sauraron hujojin daga lauyoyi, na gamsu cewa wanda ake zargin ya aikata laifin da ake tuhumarsa," in ji alkalin.

"Ina kuma ra'ayin cewa masu shigar da karar sun yi aikinsu yadda ya dace wurin gamsar da kotu cewa wanda ake zargin ya aikata laifin.

"Don haka an ayyana shi matsayin mai laifi kuma an yanke masa hukuncin kisa ta hanyar rataya."

Alkalin ya kuma yi watsi da batun cewa wanda ya aikata laifin yana da tabin hankali.

Hujojjin da aka gabatarwa kotu ya nuna cewa mai laifin ya daba wa basaraken wuka a kirji ne bayan ya zarge shi da kwace masa kujerar mulkin da ya kamata ya samu.

Mutuwar Ogunsakin a 2018 ya jefa garin cikin bakin ciki da rudani.

Lamarin ya janyo zanga-zanga daga mazauna garin da masoyan basaraken.

Shima mai laifin dan uwa ne ga marigayin sarkin, Kafin ya kai wa sarkin hari, ya zauna na dan lokaci a fadar jim kadan kafin taron majalisar masu sarauta.

Duk da cewa an kore shi, ya sake dawowa fadar bayan taron ya kuma caka wa Mr Ogunsakin wuka a kirji.

Sarkin ya rasu yayin da ake hanyar kai shi asibiti.

Mr Omoniyi ya tsere daji bayan aikata laifin amma daga bisani aka kama shi.

An nada Ogunsakin sarautar Onise na Odo a Ekiti a 1986.

Saurari karin bayani ...

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN