Jerin sunayen ministocin da suka sauka daga mukamansu domin yin takara


Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi ban-kwana da ministocinsa da suka ajiye aiki don yin takara a babban zaɓe mai zuwa na 2023. BBC ta ruwaito.

Yayin jawabinsa a ranar Juma'a, Buhari ya ce ya yi imani da yawa daga cikin ministocin na da ƙwarewar da za su iya gadarsa.

"Babu wata tantama idan aka samu shugaban ƙasa daga cikin ministocin nan za a ga cikakkiyar ƙwarewa da kuma tsabar aiki ga al'umma," in ji shi.

"Wannan na ɗaya daga cikin tarihin da za mu bar wa 'yan Najeriya."

A ranar Laraba ne Shugaba Buhari ya umarci dukkan ministoci da shugabannin hukumomi da ma'aikatu masu son tsayawa takara a muƙamai daban-daban da su ajiye ayyukansu nan da ranar Litinin mai zuwa.

Daga cikin ministocin da suka yi ban-kwana da shugaban a ranar Juma'a har da Ministan Shari'a Abubakar Malami, wanda rahotanni ke cewa zai yi takarar gwamna a jiharsa ta Kebbi.

Ministocin su ne:

Ministan Shari'a Abubakar Malami

Ministan Sufuri Rotimi Amaechi

Ministan Ƙwadago Chris Ngige

Ƙaramin Ministan Man Fetur Timpre Sylva

Ministan Neja Delta Godswill Akpabio

Ministan Kimiyya da Fasaha Ogbonnaya Onu

Ministar Harkokin Mata Pauline Tallen

Ƙaramin Ministan Ma'adanai, Uche Ogah

Ministan Kimiyya da Fasaha Ogbonnaya Onu

Ƙaramin Ministan Neja Delta Tayo Alasoadura.

Shugaba Buhari wanda ya ɗare mulki a 2015 zai kammala wa'adin mulkinsa nea watan Mayun 2023, yayin da za a yi zaɓukan ƙasar kuma a Fabrairun 2023.

Ana sa rana jam'iyyun siyasa za su gudanar da zaɓukan fitar da gwani kafin ranar 3 ga watan Yunin 2022.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN