Jarirai 11 sun babbake har lahira sakamakon tashin gobara a Asibiti a kasar Senegal


Jarirai 11 da aka haifa sun mutu a wata gobara da ta tashi a wani asibiti a yammacin birnin Tivaouane na kasar Senegal, shugaban kasar ya bayyana a yammacin Laraba 25 ga watan Mayu. 

Shugaba Macky Sall ya sanar a shafinsa na Twitter cewa jarirai 11 ne suka mutu sakamakon gobarar da ta tashi a asibitin Mame Abdou Aziz Sy Dabakh. 

"Ina cikin jimami da damuwa game da mutuwar jarirai 11 da aka haifa a gobara a sashen kula da jarirai na asibitin gwamnati," ya wallafa a shafinsa na Twitter.

Sall ya kara da cewa "Ga uwayen su da iyalansu, ina nuna matukar juyayina."

"Gobarar ta bazu cikin sauri," in ji shi.

Magajin garin Demba Diop ya ce "an ceto jarirai uku".

A cewar kafafen yada labaran kasar, an bude sabon asibitin Mame Abdou Aziz Sy Dabakh.

Ministan lafiya Abdoulaye Diouf Sarr, wanda ke birnin Geneva yana halartar wani taro da hukumar lafiya ta duniya, ya ce zai koma kasar Senegal cikin gaggawa.

"Wannan yanayin abin takaici ne sosai kuma yana da zafi," in ji shi a rediyo. "Ana gudanar da bincike don ganin abin da ya faru."

Lamarin ya kuma biyo bayan cece-kucen da kasar ta yi kan mutuwar wata mata da ke nakuda mai suna Astou Sokhna, wadda ta mutu a lokacin da rahotanni suka ce tana rokon a yi mata tiyatar Casarean a lokacin da ta shafe sa'o'i 20 tana fama da nakuda. Dan cikinta ma ya mutu.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN